Dokar majalisar, da aka kwashe shekaru 17 ana muhawara a kanta, ta raba ma'aikatar man fetur ta kasa kashi hudu.
Kashi na farko ita ce hukumar da za ta sa ido a harkokin man fetur da kula da kayyade ayyuka da walwalar ma'aikata.
Kashi na biyu zai kula da sayar da hannun jarin ma'aikatar. Kashi na uku zai duba yanayin shiyar da ake hako man da yanayin rayuwar al'ummar wurin.
Kashi na hudu zai kula da horas da ma'aikata.
Mai magana da yawun majalisar dattawa Dr Aliyu Sabi Abdullahi ya yi karin haske akan dokar. Inji shi dokar za ta tabbatar cewa cin hanci da rashawa da rufa rufa da yin watanda da dukiyar kasa duk dokar ta kawar dasu. Ya ce da mutum daya ne yake mulkin NNPC. Ita ce da dokokin hako mai, sayarwa saboda haka kamfanin sai ya ki saka kudin da ya kamata cikin asusun kasa. Inji shi kamfanin na NNPC ke da doya da wuka.
Akan abun da dokar ta tanada wa al'ummar da ake hako man daga yankin su, Sanata Abdullahi Gumel ya ce dokar za ta taba rayuwar mutanen saboda an cire hannun gwamnati kuma za ta sa mutanen waje su saka hannun jari a harkokin man kasar. Hakan zai kara ba da guraben ayyukan yi da yawa. Baicin haka arzikin kasar zai karu.
Shi ma shugaban kwamiti wucin gadi a majalisar wakilai Hassan Ado Doguwa, ya ce dokar abun alfahari ce ga kasa. A cewarsa idan an tabbatar da ita za ta kara habaka tattalin arzikin kasar, za ta kuma ba kasar wajen samun kudaden shiga masu yawa, kana za ta samar da kawanciyar hankali da natsuwa a yankunan da ake hako man domin al'ummar wurin zasu rika samun salala.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Facebook Forum