Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Borno Ya Tare A Bama, Ko Mene Ne Dalili?


Gwamnan Borno Kashim Shettima a Bama
Gwamnan Borno Kashim Shettima a Bama

Gwamnan Borno ya kai ziyarar aiki Bama ta sai abun da hali ya yi kafin ya koma fadarsa a Maiduguri domin yana son ya tabbatar komi ya kankama kafin ya bar 'yan garin su koma muhallansu

Gwamna Kashim Shettima na jahar Barno, ya ziyarci garin Bama, kuma zai yi 'yan kwanaki domin ya ga duk ayyukan da ake yi tare da tabbatar al'ummar garin zasu iya komawa muhallan su.

A cewar gwamnan, gidaje wajen dubu 11 da dari biyar an gama gina su, amma babban abun shi ne samar da ruwa. Ya ce zai zagaya kwane lungun garin ya ga cewa an gama bututun ruwan da ake tonawa. Haka ma zai tabbatar da an gyara, ko sake gina makarantu da asibitin garin.

Inji gwamnan da ya yi niyyar komawa Maiduguri bayan kwana daya amma ba zai yi hakan ba sai ya tabbatar an kammala ayyuka na musamman kamar samar da janareto, domin wadata ruwa, da haka rami kewaye da garin saboda hana 'yan ta'adda shiga garin.

An kammala gina manyan makarantun firamaren garin. Akwai wasu masu azuzuwa 30 zuwa 40. Gwamnan ya yi alkawarin samarda makamshi ta hasken rana da ake kira ( solar) a makarantun domin su samu wutar yin anfani da fanka.

Dangane da tsaron garin, gwamnan ya ce mutanen garin ne zasu yi tsaron garin su. Ya kira gare su da kada su yi sakaci, amma su yi takatsantsan, kada a bari wanda bai cancanta ba ya shiga garin.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG