Babbar Majalisar Sarakunan gargajiyar kasar Najeriya ta yi taron ta na shekara-shekara, karo na shida a Sokoto
WASHINGTON, DC —
Babbar Majalisar Sarakunan gargajiyar Najeriya ta yi babban taron ta na shida a Sokoto. Sarakunan sun tattauna ne a kan matsalolin cikin gidan da suka danganci rikicin siyasa da barazanar tsaro, da tulin kalubalen da kasa ke fuskanta, sannan kuma sun duba irin gudunmawar da za su iya bayarwa da kuma irin rawar da za su iya takawa wajen samar da saukin wadannan matsaloli. Daga bude babban taron Ibrahim Alfa Ahmed ya tuntubi wakilin Sashen Hausa a Sokoto Murtala Faruk Sanyinna ta wayar talho suka tattauna muhimman batutuwan da suka fi daukan hankulan masu jawabai:
Your browser doesn’t support HTML5