Har zuwa lokacinda muke gabatar muku da wannan labarai, ‘yan kwana kwana suna kai goro su kai mari a kokarinsu na shawo kan gobarar, amma babu alamar suna samun galaba.
Wakilinmu a legas Ladan Ibrahim Ayawa, yace gobarar wacce ta faro daga hawa na daya yanzu ta kai hawa na biyar.
Wannan babban ginin yana kunshe da kamfanoni da ‘yan kasuwa daban daban na cikin gida da wajen Najeriya. Ladan yace akwai ma Banki a cikin wanan gini.
Zuwa yanzu dai bamu sami labarin hasarar rayuka ba.