A cikin bayanin shi, Dr Gana ya fadi cewa, ciwon sankarau ciwo ne da ke faruwa a cikin al'uma a lokaci lokaci, musamman lokacin zafi. Yace, yana yiwua cutar ta yadu idan aka samu lokacin da garkuwar jikin mutane ya ragu. Ya kuma ce yawanci akan sami wanan cutar a inda mutane suke taruwa dayawa, ko ta wurin hira ko kwanciya. Yayinda mutane suke kwanciya suna numfashi da juna kuma ba da isashen iska ba, ba wuya a samu yaduwar sankarau.
Cutar sankarau tana da wani abin da ake cewa da ita Cyclical Pattern, wato cutar tana iya juyowa bayan wasu shekaru da ake tsamanin ta gama tafiya. Sankarau cuta ce mai tafiya sosai, kuma babu dama a samu cutar ta shiga kasashen da ke kusa da inda aka sami alamun ta.
Dr. Ahmed Gana ya kuma kara cewa, baban makamin da ya kamata a dauka shine rigakafi. Ya ce akwai aluran rigakafi da dama da gwamnati ta raba wa jihohi saboda kawar da cutar. Ya fadi cewa idan aka samu aka yiwa jama'a rigakafin sankarau, duk da maza, da mata, da yara tare, kuma ba sai an jira lokacin zafi ba, za a samu sauki wajen yaye cutar sankarau.
Ga cikakken bayanin Dr Ahmed Gana a hirarsu da wakilin Sashen Hausa Nasiru Elhikaya