Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Ashirin Da Bakwai Sun Rasa Rayukansu


Gawarwakin wadanda aka kashe
Gawarwakin wadanda aka kashe

Wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a garin Gulumba cikin karamar hukumar Baman jihar Borno

Cikin jihohi uku dake cikin dokar ta baci a arewa maso gabashin kasar Najeriya, jihar Borno, inda kungiyar Boko Haram ta fara kafa cibiyarta, ta fi kowace jiha fama da hare-hare da kashe-kashe da kone kone.

A jihar Bornon kanta karamar hukumar Bama tafi samun hari daga kungiyar Boko Haram. Wannan lokacin ma 'yan bindiga da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a garin Gulumba inda suka yi mummunan barna.

Kamar yadda shugaban karamar hukumar Baba Shehu Gulumba ya bayyana wa Muryar Amurka ya ce wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a garin Gulumba. Sun kona gidaje. Da zara mutum ya fito sai su harbeshi. A lokacin harin sun kashe mutane ashirin da bakwai sun kuma raunata akalla mutane goma sha biyu.

Dangane da karin barnar da suka yi Baba Shehu ya ce sun kone gidaje talatin da shaguna ashirin kana suka hallaka dabbobi dari hudu da hamsin. Basu tsaya nan ba. Sun kone buhunan hatsi fiye da dari tara da tsabar kudi kimanin nera miliyan uku da dubu dari biyar.

Bayan wannan mummunar barnar da 'yan bindigar suka haddasa Baba Shehu ya ce yanzu wasu mutanen basu da komi da zasu sa babu kuma abinci. Mutanen Gulumba sun shiga cikin halin kakanikayi. 'Yan kasuwa da dama kuka suke yi domin an karyasu.

Abun mamaki lamarin ya faru ne karfe shida na safe, wato bayan gari ya waye sarai. Kodayake jami'an tsaro sun zo daga baya amma Baba Shehu ya ce mutanen garin sun yadda yanzu su dauki kulake da bindigogi su kare kansu. Shi Baba Shehu ya ce kaninsa dake binsa yankashi 'yan bindigan suka yi. Ya ce karon farko da suka zo sun kone gidan kansa bayan sun cire duk abubuwan dake gidan kana suka cinna masa wuta.


Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye


LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”
XS
SM
MD
LG