Ta rasu ne shekara guda da ta wuce a kauyen Balmoral Castle a Scotland tana da shekaru 96.
WASHINGTON, D. C. - Bayan mutuwarta, ɗanta, Charles, ya karbi sarauta nan da nan.
Charles ya ce shi da matarsa, Camilla, za su kwashe yini guda su kadai suna tunawa da ita a gidan sarauta na Scotland.
"A wannan lokacina bikin cika shekara ta farko na rasuwar Mai Martaba da kuma hawa na karagar mulki, muna tunawa da tsawon rayuwarta, sadaukarwarta da duk yadda take a zukatun yawancinmu," in ji Sarki Charles a cikin wata sanarwa ta yanar gizo.
A ranar tunawa da mutuwarta, danginta masu sarauta sun yada wani hoton da ba a taba gani ba na Sarauniyar wanda fitaccen mai daukar hoto Cecil Beaton ya ɗauka a 1968, hoton da ya taba bayyana a cikin wasu hotuna na tarihi na Beaton.