Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Halarci Jana'izar Sarauniya Elizabeth II


Jana'izar Sarauniya Elizabeth
Jana'izar Sarauniya Elizabeth

Birtaniya da duniya sun yi bankwana na karshe ga Sarauniya Elizabeth ta biyu a jana'izar da ta sami halartar Shugabanni da Sarakuna da Firaministoci da kuma jama'a da suka yi dafifi a kan titunan birnin Landan don karrama Sarauniyar da ta shafe shekaru 70 tana mulki.

An ayyana ranar Litinin ne a matsayin ranar hutu don girmama Elizabeth, wacce ta mutu ranar 8 ga Satumba. Dubban daruruwan mutane suka yi tururuwar yi wa gawarta ganin karshe kafin rufe kofar inda gawarta take a sanyin safiyar wannan Litinin.

Sarki Charles III da mai dakinsa Camilla da sauran 'yan gidan sarautar Birtaniya sun raka gawar sarauniyar zuwa kabarinta bayan bikin jana'izar na fadar Westminster, kana an binne sarauniya a kusa da mijinta Yarima Phlip a makabartar Saint-Georges.

Tun kafin a fara hidimar, hukumomin birnin sun ce wuraren kallon da ke kan hanyar jana'izar sun cika.

An karfafa matakan tsaro a ciki da wajen birnin Landan an kuma dakatar da tashi da saukan jiragen sama a fadin kasar a wani mataki na yin tsit din mintuna biyu don karrama basarakiyar mai shekaru 96 da ta cika kwanaki 10 da suka gabata.

Bayan jana'izar, an kawo akwatin gawar - tare da rakiyar rundunonin sojoji sanye da kayan sawa da 'yan uwanta - a titunan babban birnin kasar.

XS
SM
MD
LG