Yarima Charles ya dare karagar mulkin sarautar Ingila bayan rasuwar mahaifyarsa Sarauniya Elizabeth II.
A ranar Alhamis, masarautar ta Ingila ta sanar da rasuwar Sarauniya Elizabeth sa’o’i bayan da ta sanar da cewa daddadiyar Basarakiyar tana karkashin kulawar likitoci. Ta rasu tana da shekaru 96.
Yanzu Charles wanda shi ne babban danta, ya zama Sarkin Ingila.
An haifi Sarki Charles a ranar 14 ga watan Nuwambar 1948 a fadar Buckingham.
A lokacin da mahaifiyarsa (Sarauniya Elizabeth) ta dare karagar mulki a shekarar 1952, Charles na da shekara 3.
Ya zama Prince of Wales a lokacin yana da shekaru 20.
Sarki Charles ya yi karatu a Jami’ar Cambridge Trinity College, inda a shekarar 1970 ya zama mutum na farko da yake da karatun digiri a masarautar.
Ya kwashe shekaru bakwai a matsayin sojan da ke ayarin sojojin da ke tuka jiragen masarautar, daga baya kuma ya koma fannin sojan ruwa har ya koyi yadda ake tuka jirgi mai saukar ungulu.
Ya kammala aikin soja a matsayin kwamandan Bronington a shekarar 1976.
A shekarar 1977 ya hadu da Sarauniya Diana Spencer a lokacin tana da shekaru 16 inda a watan Fabrairun shekarar 1981 suka sanar da shirinsu na yin aure.
An daura aurensu a ranar 29 ga watan Yulin 1981, wanda aka yi a Cocin Paul Cathedral, bikin da aka watsa shi ta kafar talabijin.
Kasa da shekara daya bayan auren, aka haifi Yarima William, wanda ya yanzu ya zama Yarima mai jiran gado, sannan a shekarar 1984 aka haifi kaninsa Yarima Harris.