Sakamakon Zaben Shugabannin APC Ya Bar Kura Baya

APC

Biyo bayan zaben shugabannin APC wadanda basu gamsu da sakamakon ba ka iya ficewa su shiga PDP
Rahotanni na nuna cewa wadanda basu ji dadin sakamakon zaben shuganannin jam'iyyar APC ba suna iya ficewa daga jam'iyyar su shiga PDP.

Sabon shugaban jam'iyyar John Oyegun dan yankin Neja Delta ne yankin da shugaba Jonathan ya fito, yankin dake da arzikin man fetur. Masu harsashen harkokin siyasa sun ce an zakuloshi ne domin ya samar ma APC kuri'u a zaben 2015.

Sabon sakataren jam'iyyar Mai Mala Boni yayi watsi da barakar da ake harsashen ta kunno kai a jam'iyyar ta APC. Yace masu irin wadannan maganganun mutane ne da suka tsorata ganin yadda jam'iyyar ta habaka da karfin da take dashi yanzu da kuma shirin da tayi domin karbar mulki badi. Yace shugabanninta sun nuna hikima da yadda suka gudanar da jam'iyyar har aka yi zaben shugabanninta cikin lumana.

Masanin harkokin siyasa Dr. Sadiq Abba yace bashi da tsammanin akwai wani mutum a cikin siyasa da yake neman shugabancin kasar dake da martaba da mutunci da daukaka kamar Janaral Buhari. Kiransa baba bai nuna ya tsufa ba, wato ba zai iya shugabancin kasar ba. A'a a siyasance ana nuna karbuwarsa ga mutane ne. Ana ganin shi ne kadai dattijon da zai iya gudanar da harkar kasar ta kama hanyar cigaba ta kowane fanni. Babu wani da talakawa suka sadakar da kansu da rayuwarsu gareshi irin Buhari.

Dr Abba yace akwai wasu mutane irin su Kwankwaso, El-Rufai, Oshiomole, Amaechi da ma Fashola amma samun irin Buhari zai yi wuya.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Sakamakon Zaben Shugabannin APC Ya Bar Kura Baya - 2'58"