Kakakin rundunar Mr. Victor Babayemi shi ya shaidawa manema labarai a birnin Ado Ekiti fadar gwamnatin jihar. Yace duka jami'an tsaro zasu yi aiki tare domin su tabbatar da doka da oda a lokacin zaben gwamnan jihar kana za'a sanya 'yansanda uku a kowace rumfar zabe. Ban da haka za'a baza jami'an tsaro shida ko bakwai a kowace runfar zaben.
Babayemi yace wani lokaci 'yan siyasa suna bada dariya saboda wasunsu suna da halaye da basu dace da matsayinsu ba. Yace za'a karo jami'an 'yansanda dubu biyu daga jihohi dake makwaftaka da jihar domin dakile duk wata tashin tashina a lokaci da kuma bayan zaben. Kakakin ya bayar da lambobin wayar tarho da za'a kira idan akwai matsala a koina.
Rundunar zata kuma yi anfani da jiragen sama biyu da karnukan 'yansanda da dawakin 'yansanda duk a kokarin tabbatar da doka da oda lokacin zaben da kuma bayan an kammalashi.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.