Sanatan ya rasu jiya da sanyin safiya a wani asibiti a Legas. Kafin rasuwarsa ya taba zama dan majalisar dokokin jihar Neja a shekarar 1983. Hakazalika an taba zabansa ya zama dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya a shekarar 1993. Daga bisani ya zama mataimakin darakta na jam'iyyar PDP na kasa.
Da ya koma jihar Neja ya zama sakataren gwamnatin jihar Neja a lokacin da Injiniya Abdulkadiri Kure ke gwamnan jihar. A cikin watan Afrilun 2007 ne dai aka zabeshi ya zama dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar gabashin jihar Neja.
A bangaren ilimi kuwa Sanata Dahiru Kuta yayi digirinsa na farko a Jami'ar Bayero dake Kano. Yayi kuma digiri na biyu a Jami'ar Ile-Ife.
Sanatan ya rasu ya bar mata daya da yara guda hudu. Za'a yi jana'izarsa a babban masalacin Jumma'a dake birnin Minna fadar gwamnatin jihar Neja.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.