Shahararen mai wa'azin Musulunci Sheikh Dahiru Bauchi kuma shugaban darikar Tijjaniya yace abun kunya ne. An nada sarki a Gombe ba'ayi komi ba. Sun yi abun kunyan da suka yi a Kano ne domin jam'iyyarsau ba daya ba ce da ta mutanen Kano. Abubuwa da aka boyewa zasu bayyana a fili ke nan. Da wasu abubuwa dake faruwa ana zargin akwai hannun gwamnati ciki. Yanzu an fiti faro-faro ke nan ana son a yiwa arewa wasu abu.
Abun akwai siyasa a ciki. Sun rufe filin saukar jiragen sama domin sun san sabon sarkin Sanusi Lamido Sanusi ya san mutane da yawa da suke da jiragen sama kuma zasu kawo masa gaisuwar tayashi murna. Basa son jirage su taru domin bada ra'ayinsu aka zabi sarkin ba. Yin anfani da ikon rufe filin abun kunya ne.
Sheikh Bauchi yace hakkin gwamnatin Kano ne da masu zaben sarki su zaba gwamnatin jiha kuma ta bayyana sunan wanda Allah Ya zaba. Doka ta ba gwamnatin tarayya ta nada minista amma ba sarki ba. Gwamnatin tarayya bata da ikon ta nadawa Kano sarki sai wanda aka zaba ta hanyar da aka saba. Masu zaba su zaba gwamna kuma ya zartas.
A doka ba hurumin gwamnatin tarayya ba ne. Wajen Musulmi kuma kayan Musulmi ne kuma aiki Musulmi ne. Yakamata gwamnati ta nemi zaman lafiya a bar abubuwa su gudana yadda yakamata su gudana. Gwamnatin tarayya yakamata ta bi doka ta nunawa mutanen kasa bin doka. Bai kamata gwamnati ta yi wani abu na karya doka ba ta kuma koyawa mutanen kasa karya doka ba. Hakin gwamnatin tarayya ne idan fitina ta tashi a wani wuri ta kwantar da ita amma ba ita ba ce zata nemi tayar da fitina ba a wurin da babu fitina.
Duk mai neman mutanen arewa da sharri Allah Ya mayar masa da sharrinsa a kansa. Allah Ya ba kasar lafiya da zaman lafiya.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.