Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Wanene Ya fi Cancanta Ya Shugabanci Najeriya, Buhari ko Atiku


APC
APC

Bayan jam'iyyar APC ta zabi sabbin shugabanni yanzu zaben dan takarar shugaban kasa zata fuskanta in da tuni ake kai ruwa rana akan wanda ya candcanta jam'iyyar ta tsayar.

Zaben shugabannin jam'iyyar APC ya bude wani sabon babi wa jam'iyyar lamarin da ba'a san yadda zai kasance ba.

Akwai alamu cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar zai fito ne daga arewacin kasar. Sai dai tambaya nan it ace shin wanene ya cancanta jam'iyyar ta tsayar.

Alhaji Sani Adamu shugaban wata kungiyar dake fafitikan ganin tsohon mataimakin shugaban kasa Abubakar Atiku ya zama shugaban kasa a zaben shekara ta 2015 yana ganin Atikun shi ne ya dace jam'iyyar APC ta tsayar. Yace shi ne gwanin kowa. Atiku yana cikin wadanda suka tsayar da dimokradiya a kasar. Su ne suka tabbatar da dakatar da mulkin soja. Babu wanda yakamata ya sake rike kasar idan ba Atiku ba.

Dangane da yawan canza jam'iyya da Atiku yake yi sai Sani Adamu yace mutum ne mai mutane da yawa sabili da haka duk inda mutanensa suke nan ya nufa domin ya share masu hawaye.

Akan Buhari Sani Adamu yace ai yakamata ya janye domin ya tsufa. Yace yayi kwatanci da irin hakurin da Atiku ya sha yi tun shekarar 1993. Yakamata shi Buhari ya marawa Atiku baya ne domin a samu a tafi tare.

Amma irin su Alhaji Sani Tolo tsohon sakataren jam'iyyar ANPP kuma yanzu jigo a jam'iyyar APC a jihar Taraba yana ganin Buhari shi ya fi cancanta. Yace akwai abun da kudi ba zai iya yi ba. Talakawa sun gane da can an yi anfani da su an cucesu amma yanzu wanda zai taimakesu suke so. Akwai mutane da dama irin su Kwankwaso amma wanda talakawa zasu fi yadda dashi shi ne Buhari. Idan maganar gaskiya za'a bi da kuma wanda zai kawo arewa sai Buhari. Ko bashi da kudi talakawa zasu fito su zabeshi.

Da alamu batun tsayar da dan takarar shugaban kasa ka iya kawowa jam'iyyar APC matsala kadayake sakataren yada labaran jam'iyyar a jihar Adamawa yace ba haka zancen yake ba. Yace koina a duniya idan ana takara ana tada jijiyar wuya.

Ga cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz.
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG