Da yake yiwa sashin Hausa na Muryar Amurka Karin bayani kan wannan sabuwar manufa, daraktan watsa labarai na babban bankin Mr. Isack Okorafor yace an dauki matakinne saboda mutane na korafin shan wahala wajen samun kudaden musaya, saboda haka yanzu idan aka bari Naira ta samawa kanta daraja a kasuwa zai zaburadda da darajarta.
Kwararru kan tattalin Arziki irinsu Alhaji Muhammadu Mustapha Bintube, dake zaman tsohon Babban manajan Daraktan Bankin JAIZ na farko a Najeriya, ya ce wannan tsarine mai kyau, domin zai sa masu zuba jari su tuttudo cikin kasar kana samun kudaden musaya zaiyi sauki, al'amarin da yace zai karfafa bubbude masana'antu da hakan zai samarwa matasa a kasar aikinyi, to sai dai kuma Alhaji Bintube, yayi gargadin cewa dole yan Najeriya su jure yar wahalar da za a sha na dan karamin lokaci kafin a ci moriyar abin daga karshe.
A bangarensu, yan kasuwa a kasar na cewa yanzu babu abin da zasuce sai sunga yadda ta kaya, Alhaji Isa, sakatare dake zaman daya daga cikin shugabannin yan kasuwa a kasar yace koda suna ga babban bankin ya dau wannan mataki da kyakkyawan niyya to amma zasu sa ido suga in manufar bata haifarwa tattalin arzikin da mai ido ba, to dole a canza lale.
Your browser doesn’t support HTML5