Sanata Ali Wakili mai wakiltar Bauchi ta Kudu yace sun yi zama ne akan dokar da majalisa ta yi na kafa hukumar inda wasu sanatoci suka ga bai dace a sa hekwatar a Abuja ba.
Sanatocin sun ce an kafa hukumar ce domin ta gyara jihohin arewa maso gabas musamman wadanda rikicin Boko Haram ya fi shafa. Suka ce kamata yayi a kai hedkwatar cikin yankin da zata yi aiki. Sanata Wakili yace dalili ke nan da shi ma yace a kaita Bauchi.
To saidai wasu ma da suka fito daga jihar Borno suna ganin jihar ce ta dace a kai hedkwatar domin itace kungiyar Boko Haram ta fi yiwa kaca kaca. Nan aka haifi kungiyar, nan kuma ta yi kakagida nan kuma ta fi yin barna.
A kan ya kamata sanatocin da suka fito daga yankin su cimma matsaya guda sai Sanata Ali Wakili yace abu ne wanda za'a iya cimma matsaya amma kuma abu ne na al'umma. Yace hakkin kowane ya fadi ra'ayin al'ummarsa. Amma tunda yake abu ne na jama'a wadanda suka fi rinjaye su za'a bi.
Yanzu dai majalisar dattawa ta kafa kwamiti mai mutane shida domin warware matsalar.
Amma wani bincike ya nuna cewa shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Sanata Ali Ndume ya shawarci sanatocin arewa maso gabas din da su tattauna tsakaninsu domin cimma matsaya kan jihar da ta cancanci zama hedkwatar hukumar.
A wata sabuwa kuma kakakin majalisar wakilai Barrister Yakubu Dogara ya bayyana tsoronsa kan yadda wasu kungiyoyi masu zaman kansu ke neman kudade da sunan zasu taimakawa al'ummar arewa maso gabas. Yace saidai basu san inda kudaden suke shiga ba. Yace saboda haka idan aka kafa hukumar raya yankin zata yi maganin irin wadannan kungiyoyin.
Ga karin bayani.