Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram Ta Bude Gidan Radiyo


Suna watsa shirye shiryen su a zangon FM, akan mita 96.8

Kungiyar Boko haram sun bude wani tashar radiyo na FM, wanda suke watsa farfaganda na kalubalatar kasashen dake yaki dasu ke fadi na cewa ana samun galaba akansu, wannan gidan radiyo dai an kafa shine garin Tolkomari a jihar arewa mai nisa kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru.

Suna watsa shirye shiryen su a zangon FM, akan mita 96.8, jama’a a garin na Tolkomari, sun ce suna kamo tashar wannan gidan radiyo.

Wannan lamari dai yan ciwa gwamnatin kasar ta Kamaru tuwo a kwarya domin gano inda ‘yan kungiyar ta Boko Haram, ke watsa shirye shiryen su, amma masu iya Magana na cewa idan aka juri zuwa kogi da tulu wata rana za’a dawo da gammo.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG