Ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya taka rawa sosai tare da wata cibiyar Amurka ta kasa da kasa kan tsaro da sharia' a bada wannan horo da ya kunshi hafsoshi daga sojojin Najeriya na kasa, ruwa da na sama.
Horon kazalika na wani bangare na hobbasan hedkwatar tsaron Najeriya
wajen kara inganta alakar sojoji da fararen hula musamman yayin da
sojojin ke wani aikin samar da tsaro a cikin gida.
Wannan hobbasa kazalika na a matsayin wani bangare na yunkurin kara irin rawar da masana shari'a ke takawa wajen daukar matakin duk wani fafatawa da za a yi da kuma bada muhimmanci wajen kare hakkin dan adam da ma kare fararen hular.
An dai dudduba irin darussan da Amurka ta koya a yake yaken da tayi da nufin zama izina yayin tura sojoji zuwa duk wani aikin samar da tsaro, inda aka duba dokoki da ka'idojin da sojoji ke amfani da su da nufin ganin ba a sa rayuwar fararen hula cikin hatsari ba.
Amurka da Najeriya dai na aiki tare wajen ganin ana bin ka'idoji da tanade tanaden dokokin gidan soja da kuma ya dace da tsarin kare mutanen da basu san hawa ba balle sauka yayin da dakaru ke tsarawa da kuma fafatawa a aikin samar da tsaro.
A baya dai Najeriya ta sha suka kan yadda akai yi ta zargin jami'an tsaronta da yiwa hakkin dan adam karan tsaye musamman yayin da dakarun ke fafutukar kawo karshen 'yan ta'addan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar da kuma kudu maso gabashin kasar inda masu rajin ballewa daga kasar ke tada tunzuri.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5