A Najeriya daidai lokacin da rundunar sojin kasar ke kara karfafa gwiwar mayakanta, su kuwa ‘yan bindiga suna ci gaba da gallazawa jama'a.
Wannan na faruwa ne lokacin da ‘yan bindiga suka kashe mutun biyar da yin garkuwa da wasu 4, bayan ziyarar da babban hafsan soji ya kai a Sokoto.
‘Yan Najeriya musamman a yankunan arewa na ci gaba da fuskantar barazana daga ‘yan bindiga daidai lokacin da mahukumta ke kara matsa kaimi wajen magance matsalolin rashin tsaro a yankunan.
Mutanen kauyen Idikki a yankin mazabar Rungumawar gaci a karamar hukumar Illela mai iyaka da garin Konni na Jamhuriyar Nijar sun wayi gari ranar alhamis cikin tashin hankali inda mahara suka afkawa garin da asubahi.
Dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar yankin Bello Isa Ambarura ya bayyana yadda lamarin ya faru.
Wannan harin ya zo ne lokacin da babban hafsan mayakan Najeriya Lt Gen Faruk Yahaya yake ziyarar karfafa gwiwar dakarun da ke fagen daga da kuma kiyasin nasarorin da aka samu a Jihohin arewa maso yamma.
“Goron sallah da za ku ba ni shi ne ku kara kashe wadannan ‘yan ta'adda, ‘yan fashin daji da kuma masu garkuwa da mutane a ko’ina cikin fadin kasar nan.
Ina karfafa gwiwarku duka kada ku yi kasa a gwiwa ku ci gaba da yakar wadannan mutanen a wuraren da suke boye, kada ku daina yakar su har sai kun ga baya gare su duka kuma ku kawo min makaman su” Faruk ya ce.
Baya ga kayan aikin da yake sheda musu za'a kara samar musu, hakama an dauki matakai na kyautata jin dadin su inda har an kaddamar da bude gidajen soji da aka samar a garin Zuru ta jihar kebbi baya ga aza tubalin ginin sabuwar barikin soji a Sokoto.
Na yi kokarin jin ta bakin rundunar 'yan sandan Najeriya akan harin da aka kai a garin Iddiki amma dai abin ya ci tura.
‘Yan Najeriya dai na ci gaba da nuna fatar cikar alkawali da shugaban Najeriya yayi na kawar da matsalolin rashin tsaro kafin ya mika mulki ga sabuwar gwamnati.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir: