ABUJA, NIGERIA- A wani yunkuri na inganta dangantakarta da al’ummar kasa, rundunar sojin Najeriya karkashin sashin harkokin farar hula na rundunar ta bayyana cewa sojin kasar ta samu rahotanni tare da daukar matakai akan korafe karafen take hakkin dan’adam sama da 500 da jami’anta suka yi cikin shekaru 6.
Hakan na zuwa ne yayin wata ganawa da sashin ya yi da 'yan jaridu kan kulla kyakyyawar dangataka da kafofin watsa labarai don taka rawa wajen magance matsalolin tsaro a kasar.
A baya dai wasu kungiyoyin kare hakkin dan’ adam irin su Amnesty International da 'yan Najeriya sun sha zargin rundunar soji kasar da cin zarafin farar hula, batun da Shugaban sashin harkokin farin hula na rundunar sojin kasar Manjo Janar Markus Kangye ya yi karin haske game da wannan bangare da ke karkashin sashinsa wanda ke kula da korafe-korafen farar hula kan sojin kasar.
"An kafa wannan bangare domin magance take hakkin bil’adama da ake zargin sojoji da aikatawa a lokacin ayyukansu na tsaron cikin gida da yaki da ta’addanci da ta da kayar baya a Najeriya, wanda a cewar ya kasance wani muhimmin ci gaba da aka samu tun daga shekarar 2016."
Ya kuma kara cewa sai an yi kwakkwaran bincike kan dukkan korafe-korafe da ake samu, kuma a lokuta da dama wasu na da inganci yayin da wasu ba su da shi
Alkaluman da sashin ya bayar sun yi nuni da cewa an samu nasarori a korafe-korafe kan jami’an sojin kasar bisa zargin take hakin dan adam, lamarin da aka danganta da yawan tarukan wayar da kan jama’a kan sanin tasirin wannan bangare na sashin farar hula na rundunar sojin Najeriya.
Birgediya janar Ojogbane Adegbe, Daraktan a fannin ayyukan sanin halayan dan Adam na sashin ya ce "sojojin da muke turawa ko suke aiki a bangaren ba sa saka kayan aiki, don muna son jama’a da suke da wani korafi kan jami’an mu su iya zuwa ba tare da sun ji tsoro ba kuma duk wanda ya je wajen ba zai gane cewa jami’an soji ba ne amma dukkan masu aiki a wajen sojoji ne."
Sanin muhimmacin rawar da kafafen watsa labarai ke takawa wajen magance matsalar tsaro musaman ma ga yadda jami’an tsaron suke gudanar da ayyukansu, ya sa sashin farar hula na sojin kasar bullo da dabarun inganta dangataka dake tsakani kamar yadda tsohon Birgediya Janar Usman kuka sheka ya ba shawara
Wannan dai shi ne kwatan farko da sashin farar hula na rundunar sojin kasar ke irin taron karawa juna sani da kafafen watsa labarai don inganta dangantaka al’umma farar hula da rundunar soji kasar.
Saurari cikakken Rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim daga Abuja