ABUJA, NIGERIA - Wannan ya biyo bayan kudirin da kungiyar ECOWAS ta dauka na yiwuwar yin amfani da karfin soja wajen maido da zababbiyar gwamnatin farar hula kan mulki a Nijar.
Tunda farko dai shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta kasashen yammacin Afirka Mousa Traore ya fada a birnin Abuja jim kadan bayan taron shugabannin kasashen yankin cewa har yanzun su a hukumance Mohamed Bazoum ne Shugaban Nijar.
Sabodahaka dole ne nan da mako daya da a koma tsarin mulkii ko ai amfani da karfin soja don maido da Shugaba Bazoum kan mulki
Akan haka a cewar Traore tuni har an umarci manyan hafsoshin rundunonin tsaron kasashen yankin da su gana don shirin tunkarar sojojin da sukai yi juyin mulkin.
A cewar kuma babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron Najeriya Janaral CG Musa ya ce a bangarensu a shirye suke don tunkarar masu juyin mulkin a Nijar da kuma dawo da zababbiyar gwamnatin farar hula da jama'a suka zaba.
To sai dai kuma, masu fafutuka a Najeriya irin su Basharu Altine Guyawa Isa na cewa ya kamata afa yi taka tsantsan domin amfani da karfin soja zai kara fadada rikicin ne.
Basharu Altine na cewa afkawa Nijar da karfin soji baya ga tarwatsa yankin kazalika zai kuma kara girma da tabarbarewar tsaro a Najeriya ne.
Saurari ciakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5