Bayan da suka gana da tsohon hafsan hafsoshin Nijar Janar Salifou Modi, Shugaban Chadi, Janar Mahamat Deby, ya gana da jagoran sojojin da suka yi juyin mulki, Janar Abdourahamane Tchiani da kuma hambararen shugaban kasar Mohamed Bazoum a inda ya ke tsare.
Haka kuma shugaba Deby ya gana da tsohon shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou, kafin daga bisani ya sake ganawa da Janar Tchani a karo na biyu donin yi masa bankwana.
Shugaban na Chadi ya yi amfani da wannan ziyara domin duba hanyoyin sasanta bangarorin da ke takun saka bayan juyin mulkin da soja suka yi a Nijer.
Hotunan da aka yada a kafafen sada zumunta na nuna Bazoum Mohamed, ya na murmushi alamar ya na cikin koshin lafiya.
A karshen taron da suka yi a ranar Lahadi 30 ga watan Yulin 2023 a Abuja, shugabanin kasashen Afrika ta yamma mambobin ECOWAS sun bai wa sojojin Nijer wa'adin mako 1 su mai da hambararen shugaban akan karagar mulki ko kuma a kore su da karfin soja.
Sojojin kasar a karkashin jagorancin Janar Abdurahamane Tchiani suka gudanar da juyin mulkin a cikin wannan makon.
Dandalin Mu Tattauna