Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Sun Gargadi Faransa Kan Shirin Kubutar Da Bazoum


Janar Abdouramane Tchiani
Janar Abdouramane Tchiani

Rundunar sojan Nijar da ta kwace mulki a makon da ya gabata tare da hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum, ta zargi gwamnatin hambararren shugaban kasar da bai wa Faransa izinin kai hari akan fadar shugaban kasar domin kokarin kubutar da Bazoum.

WASHINGTON, D.C. - Rundunar sojin da ta killace Bazoum a fadar Shugaban kasa tun daga ranar Laraba, a baya ta yi gargadi kan yunkurin fitar da shi da kasashen waje yi, inda ta ce hakan zai haifar da hatsaniya.

Nijar
Nijar

Kalaman na sojojin sun fito ne daga bakin Kanar Amadou Abdramane, daya daga cikin wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin a gidan talabijin na kasar a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ya ce Ministan harkokin wajen Nijar Hassoumi Massoudou ne ya sanya hannu a matsayinsa na Firai Minista.

An kasa samun Massoudou don tabbatar da hakan. Faransa ta yi Allah wadai da juyin mulkin tare da yin kira da a maido da Bazoum akan mulki amma ba ta sanar da wani shiri na tsoma baki ta hanyar soji ba.

Nijar
Nijar

Paris ba ta ba da amsa kai tsaye ga buƙatun yin wani bayani ba ranar Litinin.

Juyin mulkin da aka yi a Nijar ya biyo bayan mamayar da sojoji suka yi a makwabciyarta Mali da Burkina Faso a cikin shekaru biyu da suka gabata, wadanda suka biyo bayan nuna kyama ga Faransa.

Kasar Faransa dai na da sojoji a yankin na tsawon shekaru gom, wadanda suke taimakawa wajen yaki da 'yan ta'adda, sai dai wasu mazauna yankin sun ce suna son tsohuwar mulkin mallaka da ta daina tsoma baki a harkokinsu.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron

Magoya bayan gwamnatin mulkin sojan kasar sun kona tutocin kasar Faransa tare da kai hari kan ofishin jakadancin kasar da ke Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar a ranar Lahadin da ta gabata, inda ‘yan sanda suka yi feshin hayaki mai sa hawaye. A wata sanarwa ta gwamnatin mulkin soji, ta zargi Faransa da harbin masu zanga-zangar tare da raunata mutum shida.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron dai ya ce duk wani harin da aka kai kan muradun Faransa a Nijar za a mayar da martani cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

-Reuters

Ga wani karin rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Sun Gargadi Faransa Kan Shirin Kubutar Da Bazoum .MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG