Ma'aikacin jinkan da ke aiki da wata kungiyar agaji ta kasa da kasa, tun a farkon wannan shekara ne kungiyar ISWAP ta sace shi daga yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Kakakin MNJTF Kanar mohammed Dole, ya ce ma'aikacin jinkan da ISWAP ta ke garkuwa da shi a tungarta dake zirin Tafkin Chadi, an kubutar da shi ne bayan wani mummunan farmaki da dakarun su suka kai da jiragen yaki, hade da ruwan boma bomai da rokoki a tungar yan ta'addan.
Hakan ya sa yan ta'addar suka tarwatse ta yadda mutanen ake garkuwa da su kowa ya kama gabansa. A wannan yanayi ne ma'aikacin jinkan ya tsere zuwa kasar Nijar, inda dakarun MNJTF suka karbeshi.
Bayan da aka duba lafiyarsa, hedikwatar sojojin kawancen ta tura jirginta mai saukar ungulu, inda aka dauke shi aka mayar da shi gida Najeriya.
Kungiyogin agaji dai sun nuna jin dadinsu bisa wannan ci gaba da aka samu. Dakta Sake Abba, na kungiyar agaji ta Smile Medical Mission dake aiki a shiyyar ya ce wannan labari mai karfafa gwiwa.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5