Muhammadu Sanusi na biyu wanda ke ganawa da al'umma daban-daban a Kaduna bayan kwashe dogon lokaci a jahar Ikko, ya bayyana cewa, shi ne jika na farko a tarihin masarautar Kano da Allah Ya bashi sarauta. Yace "in dai an yarda cewa, Allah ba ya zalunci, to duk abinda ya same ka idan dai baka zalunci gwamnati ko ‘yan uwanka ko kuma al’umma ba, ba kuma za a iya cewa ga abinda ka yi ba, sai ka godewa Allah "
Tsohon sarkin ya ce abinda ya sa bai yi magana ba shine sanin cewa, "daukaka ake nema, ba mulki ba." Yace "Allah ne ke bada mulki ga wanda Ya ga dama, saboda haka idan Ya bada mulki sai a gode masa." Tsohon sarkin ya bayyana godiya da kaunar da yace al'umar Kano ta nuna mashi, ya kuma ce ‘yana tare da su’.
Muhammadu Sanusi na biyu ya ce idan ya yi fushi sabili da an cire shi daga sarauta ya yi wa Allah butulci, saboda yana iya hana shi mulki tun da farko yana kuma iya daukar ranshi a maimakon sauke shi daga mulki. Yace kasancewa Allah Ya bar shi da rai da lafiya da kuma iyalinshi, ya isa abin godiya.
Tsohon sarkin Kanon ya kuma ce, sarauta rai ne da ita, saboda haka mutum baya wuce ranar da Allah Ya dibar mashi, amma ba domin ikon gwamnati ba. Yace a cikin shekaru dari biyu, an yi mutane dubbai amma Allah bai basu mulki ba har da mahaifinshi da yake dan Sarki. Ya bayyana cewa ya sauke hakin al’umma dake wuyansa iyaka iyawarsa a cikin shekaru shida da ya yi yana mulki. Yana mai cewa…
"Zuri’ar Dabo mutum nawa ne, a cikin mutum dubban nan cikin shekara dari biyu, ni ne na goma sha biyu kadai a cikin dubbai da Allah Ya ba. Bai ba mahaifina ba kuma dan sarki ne. Bai taba ba wani jika ba, ni Ya fara baiwa wani jika …to banda ka gode masa har ka mutu, me za ka ce wa Allah?"
Gwamnatin Jihar Kano Ta Sauke Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi
Mai Martaba Sarkin Kano Na Fuskantar Wasu Sabbin Zarge-zarge
Rikicin Gwamnati Da Masarautar Kano Na Kara Rincabewa
A cikin jawabansu, malaman Sunnan karkashin jagorancin Sheik Adam Koki da Sheik Aminu Ibrahim Daurawa, sun bayyana cewa, sarauta da matsayi da kuma dajarar kujerar Sarauta tana bin mutum ne, ba kujera ba, suka kuma bayyana cewa al’ummar jihar Kano tana matukar kaunar Muhammadu Sanusi na biyu tare da yi mashi fatar alheri.
A ranar Lahadin da ta gabata ne Muhammadu Sanusi II ya ziyarci gwamnan jihar Kaduna Nasiru Ahmed El-rufai domin nuna godiya game da makaman da ya bashi bayan gwamnan Kano ya cire shi.
Dangantaka tsakanin tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ta yi tsami tun shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai.
Magoya bayan tsohon Sarkin sun hakikanta cewa, an sauke shi daga sarauta ne sabili da rashin goyon bayan sake zaben Ganduje bara, zargin da gwamnatin jihar Kano ta musanta.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sauke Muhammadu Sanusi daga sarauta ranar tara ga watan Maris na shekara ta dubu biyu da ishirin bisa zargin cewa tsohon sarkin ya sabawa wani sashi na dokokin masarautar Kano.
An dai nada Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin Sarkin Kano ne a ranar takwas ga watan Yunin shekarar 2014, bayan rasuwar kawunsa Ado Bayero. Kafin hawanshi kujerar sarautar, ya yi aiki a matsayin shugaban babban bankin Najeriya daga shekarar 2009 zuwa 2014 karkashin mulkin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.
Muhammadu Sanusi na biyu yana yawan magana kan batutuwa da suka shafi harkokin mulki, tattalin arziki da rayuwar al’umma da ya hada da batun aure da zaman gida.
Saurari rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti
Facebook Forum