Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Muhawara Kan Sabuwar Dokar Rajistar Wuraren Ibada a Najeriya


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Kungiyar SERAP mai fafutukan kare hakkin bil’adama da cibagan tattalin arzikin kasa da ake kira SERAP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari daya tsawata wa Ministan Shariar Najeriya Abubakar Malami da kuma Babban Darakta a hukumar rajistar kanfanoni da su dakatar da shirin fara rajistar wuraren ibada.

A cewar kungiyar ta SERAP wannan mataki tamkar tauye hakkin bil’adama ne kamar yadda yake kunshe a kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kafin kungiyoyin kare hakkin bil’adama su koka game da wannan mataki na gwamnati, tuni shugabannin addinai daban daban suma suka gabatar da kukansu ga gwamnatin ta Buhari, cewar a sake mayar wa 'yan Majalisa wannan dokar domin dubawa da kuma amincewa da ita, ta yadda ba za ta yi karo da 'yancin da tsarin mulkin kasa ya bayar ba na addini da walwala.

Pastor Yohanna Buro shugaban kiristoci ne a jihar Kaduna daya shaida wa wakilin Muryar Amurka cewa wannan doka ba ta da tushe balle makama, saidai idan gwamnati tana neman hana ibada ne ko saka takunkumi. Akwai kamata yayi tayi anfani da hanyoyin ta wajen saka ido da bibiyan duk masu karya doka ba tare da saka wata sabuwar doka ba.

Shi ma a bangarensa, Dr Bashir Yankuzo, limamin jami’ar kimiyya dake Minna ya ce koda yake babu laifi gwamnati ta saka ido ga kanfanonin da kungiyoyi domin tsaron kasa, amma hakan ba yana nufin tsaurarawa ta yarda za’a tauyen yancin wani ba ko wasu ba.

Yanzu dai abin jira a gani shine ko gwamnati zata saurari wannan kuka na jama’a.

Saurari cikakken yananin Baban Gida Jibrin a Sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG