Al-umar garin Udawa da kewaye sun ce hare-haren 'yan bindiga ya hana su noma, yanzu kuma ya na neman hana karatun boko. Yawan hare-haren kuma ya sa mafi a kasarin mutane yin gudun hijira.
Mazauna yankin shun shaidawa sashen Hausa na Muryar Amurka cewa, akwai wasu mutane masu yawa da ‘yan bindigar suka garkuwa da su a baya, amma tsawon watanni har yanzu babu labarinsu duk da cewa an biya kudaden fansa ma wasu.
Hare-haren 'yan bindiga a wasu yankunan jihar Kaduna, ya hana al'umomin yankunan sukuni. Amma gwamnatin jahar Kaduna ta ce, ta na dukkan mai yiwuwa dan kawo karshen wadannan hare-hare, a cewar kwamishinan tsaro da karkokin cikin gida Malam Samuel Aruwan.
Ayyukan 'yan bindiga a yankunan karkara ya hana manoma da dama zuwa gona, wanda wasu ke fargabar zai iya haifar da karancin abinci a Najeriya.
Domin karin bayani saurari rahotan Isah Lawal Ikara.
Facebook Forum