Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Femi Fani-Kayode Ya Bayar Da Hakuri Kan Zagin Wani Dan Jarida Da Ya Yi


Femi Fani-Kayode, tsohon ministan harkokin sufuri a Najeriya
Femi Fani-Kayode, tsohon ministan harkokin sufuri a Najeriya

Tsohon Ministan Harkokin Sufurin jiragen sama a Najeriya, Femi Fani-Kayode ya bayar da hakuri kan zagin wani dan jaridar Daily Trust da ya yi.

A cikin wani sakon da Fani-Kayode ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce, "Na janye kalmomin da na yi amfani da su kan wani dan jarida. Ina da abokai 'yan jarida da dama da kalmomina suka fusatar. Na yi nadama sosai."

Sai dai tsohon Ministan ya musanta zarge-zargen da ke cewa zai sa a ci zarafin dan jaridar na Daily Trust.

"Na yi imanin cewa ba abinda aka yi wa dan jaridar kuma ni ban aika kowa ya ci zarafinsa ba. Duk wanda ya ce an yi hakan to karya yake yi."

A cewar Fani-Kayode, ya yi shekara 30 yana aiki da 'yan jarida kuma yana daga cikin wadanda suka yi fafutukar samun 'yancin fadin albarkacin baki saboda haka ba zai taba cin zarafin kowane dan jarida ba.

Hakan dai duk na faruwa bayan da ya sha matukar suka daga 'yan Najeriya da dama kan shafukan sada zumunta sakamakon abinda ya yi.

An yi ta yada faifen bidiyon faruwar lamarin kan intanet inda aka ga yadda ya za-zage dan jaridar yayin da shi kuma ya rinka ba tsohon ministan hakuri.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG