Faransa Ta Soma Kwashe Sojojinta Daga Nijar

Dakarun Tsaron Faransa a Nijar

Rukunin farko na sojojin Faransa sun fice daga Nijar zuwa gida bayan shafe watanni sama da 2 ana kace -nace akan wannan batu da ya haifar da tankiyar diflomasiyya tsakanin sojojin juyin mulkin 26 ga watan Yuli da hukumomin Faransa.

Rukunin farko na sojojin Faransa ya fice daga Nijar zuwa gida bayan shafe watanni sama da 2 a na kace-nace wanda ya haifar da tankiyar diflomasiya a tsakanin sojojin juyin mulkin 26 ga watan Yuli da hukumomin Faransa. Sai dai wasu ‘yan kasar ta Nijar na cewa kokowa ba ta kare ba.

Sojojin Faransa a kalla 50 ne suka tashi daga filin jirgin saman Yamai zuwa gida a wannan Litinin 9 ga watan Oktoba a matsayin rukunin farko na dakaru 1500 da Faransar ta girke a Nijer tun a shekarar 2015 da sunan yaki da ta’addanci a yankin Sahel.

Haka kuma tsarin jadawalin aiyukan kwashe dakarun na nunin a wannan Talata ma wani rukunin sojojin zai kama hanya ta kasa daga birnin Yamai zuwa jihar Diffa don tsallakawa kasar Chadi kafin su shiga kasar Kamaru a kokarin neman gabar teku, abin da daya daga cikin masu hamayya da zaman sojan Faransa a Nijer Bana Ibrahim ya ayyana a matsayin wani matakin nasara koda yake a cewarsa kokowa ba ta kare ba.

A tsakiyar makon jiya ne kwamandojojin Sojan Nijar da takwarorinsu na Faransa suka yi mahada a Zinder don shata tsarin jadawali da matakan da za'a yi amfani da su wajen gudanar da ayukan kwashe sojojin na Faransa.

Masani akan sha’anin tsaro da difloamsiya Moustapha Abdoulaye ya gargadi mahukunta da ma al’ummar Nijar akan bukatar nuna halin dattako a tsawon wannan lokaci na ficewar dakarun Faransa.

Sai dai kuma ya ce a zuba ido akan dukkan ayyukan da ke da nasaba da wannan al’amari ya zama wajibi.

A washe garin juyin mulkin 26 ga watan Yuli ne majalissar CNSP ta sanar da tsinke huldar ayyukan soja da Faransa ta kuma ba kasar mulkin mallakar wa’adin wata 1 don kwashe dakarunta 1500 da ke da sansani a birnin Yamai da Ouallam bukatar da shugaba Macron ya yi watsi da ita saboda rashin yarda da halaccin hukumomin kasar ta Nijar, ya na mai jaddada cewa shugaba Mohamed Bazoum ne ke da hurumi akan zaman sojan Faransa a Nijar ko ficewarsu kafin ya bada kai bori ya hau a karshen watan satumba.

Komai na aiyukan kwashe wadanan sojoji zai kammala kafin karshen watan disamban 2023 a cewar shugaban kasar Faransa.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Rukunin Farko Na Dakarun Faransa Ya Fice Daga Nijer