Yanzu haka dai rikicin shugabanci a majilisar dokokin jihar Neja na kara zafafa biyo bayan tsige kakakin majilisar da yan majilsar suka yi a makon jiya.
Tun a makon jiya ne dai yan sanda suka rufe majilisar bayan da suka fatattaki sabbin shugabannin majilisar da barkonon tsohuwa a lokavin da suka zo domin gudanar da wani zama ranar wannan talata ne dai sabon kakakin majilisar Honarabul Isah Kawu yayi kiran taron manema labarai, inda yayi kira ga rundunar yan sanda da su bar musu harabar majilisar, kana yaja kunnen tsohon kakakin majilisar da ya daina ayyana kansa a matsayin kakakin majilisar
‘’Muna kira ga kwamishinan yan sanda na jihar Niger da ya janye yan sanda da ya tura harabar majilisar wanda ya hana su aikin su, Magana ta biyu shine shi tsohon kakakin majilisa muna da labarin cewa yana Magana kamar har yanzu shine shugaban majilisa, to don haka muna ja masa kunne ya bar wannan mambobi 20 daga cikin 25 sun yarda da tsige shi, kuma sun tsige shi kuma ya tsigu”
Sai dai da aka kira kwamishinan yan sanda Mr Olusola Amore kan wannan batu sai yace suna harabar ne bisa umurnin kotu.
‘’Umurnin kotu shine tace kar yan majilisa su tsige kakakin majilisar Adamu Usman, shi wannan Adamu Usman ne yace akwai bukatar a samar da tsaro a majilisar’’
Shima Adamu usmandin an tuntube shi game da wannan badakalar kuma ya jaddada matsayin sa cewa, har yanzu shine kakakin majilisar.
‘’Har yanzu a yadda take a gaban doka nine shugaba majilisar dokokin jihar Niger Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5