Dan jaridan na Muryar Jamus ya tambayi shugaban Chadi Idris Derby akan ko gaskiya ne akwai sojojin haya da aka dauko daga Afirka ta Kudu domin a yaki kungiyar Boko Haram.
Kodayake shugaba Idris Derby ya nuna rashin sanin labarin amma bisa ga duka alamu tambayar bata yiwa shugaban Najeriya mai barin gado dadi ba domin tuni ya bada umurnin a kwace takardun izinin shiga fadar gwamnati na dan jaridar tare da hanashi shiga fadar har na illa masha allahu.
Wakilin Muryar Amurka ya tuntubi dan jaridan Malam Ubale Musa domin a ji tasirin matakin da shugaba Jonathan ya dauka a kanshi. Yace shi a ganinsa kamar alama ce dake cikin zukatan mahukuntan tarayyar Najeriya da suke ikirarin su masu dimokradiya ne kuma sun san abun da ake kira dimokradiya.
To amma kuma ita dimokradiya ita ce 'yancin fadan albarkacin baki komai daci. Kuma gidan jarida shi ne wuri mafi cancanta inda za'a bayyana ra'ayin jama'a. Yace saboda haka tambayar da ya yi wadda an dade ana magana a kanta cewa sojojin Afirka ta Kudu aka dauko haya kuma su ne suke yakan 'yan Boko Haram ba sojojin Najeriya ba. Yace wai har suna neman a kara masu kudi inda kuma ba haka ba zasu janye, wato zasu daina yakar 'yan Boko Haram din. Idan kuma suka janye abun zai kara rincabewa.
Ubale Musa yace na daya ma abun da yakamata a tambayi shugabannin Najeriya da na Chadi shi ne shin me ake ciki ne ko kuma menen dangantakarsu da sojojin haya daga Afirka ta Kudu. Shi shugaba Derby yace shi bai san da maganar ba duk da an dade ana rade-radinta. Yace shi a wurinsa ba wani abu ba ne da ba za'a yi maganarsa ba domin a fili maganar take. Amma sabili da ana son a boye ba'a son mutanen kasa su san abun da ake ciki shi ya sa Shugaba Jonathan ya dauki matakin da ya dauka.
Ubale Musa yace abun da ya faru bai dameshi ba domin kasar da take kokarin bin tafarkin dimokradiya dole a samu hali irin na mukin kama karya wani lokacin. Amma a hankali a hankali mutane zasu tashi su ce sun ki da halin kama karya. Babbar nasara ita ce yadda mutanen Najeriya suka ki shugaba Jonathan. Wata alama ce da ta nuna mutanen Najeriya sun tashi su kwato 'yancinsu daga mulki kama karya kuma ashirye suke su tabbatar hakan ya tabbata ko menene zai faru.
Ubale Musa yace a matsayinsa na dan jarida zai yi aikinsa tsakninsa da Allah. Duk da matakin da Shugaba Jonathan ya dauka a kansa zai cigab da fadan gaskiya akansa cikin 'yan kwanakin da suka rage masa a kan kujerar shugabancin kasar. Aikin jarida baya son nuna son zuciya ko son kai ko nuna banbanci.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.