Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Jihar Bauchi Zasu Fara Yajin Aikin Sai Baba ya Gani


Da karfe sha biyun dare ne za a fara yajin aiki a jihar Bauchi, biyo bayan kasa sasantawa da aka yi tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago kan batun albashin Ma'aikata na watanni biyu da ba biya ba.

Kungiyar kwadagon jihar Bauchi tayi taron manema labarai yau don fadawa gwamnatin jihar cewa zata kaddamar da yajin aikin illa masha Allahu har sai an biya masu bukatar su, na albashin watanni biyu.

Komred Hashimu Mohammed, shugaban kungiyar gwadagon jihar yace, suna kira ga dukan ma’aikatan jihar Bauchi su zauna a gida har sai Baba ya gani, saboda tattaunawar da aka yi da gwamanti ta ci tura.

Shima shugaban kungiyar ‘yan jaridar na jihar Bauchi Dahiru Garba Mohammed, yace a tsakiyar daren yau ne za a rufe kafofin yada labarai mallakar jihar. A nashi jawabin kuma, shugaban ma’aikatan jihar Bauchi cewa yayi ma’aikatan jihar na bin bashin albashin wata daya ne ba watanni biyu ba.

Yanzu dai ya rage ‘yan kwanaki kadan a mika mulki ga sabuwar gwamnati, abinda wasu suka nuna rashin jin dadin su ganin yadda abubuwa ke wakana a jihar musamman ma dangane da yajin aikin da za a yi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG