Usman Mohammed masanin harkokin siyasa, Malami kuma a Tsangayar koyar da ‘yan majalisu dake birnin tarayya Abuja yayi maraba da wannan dokar da shugaban mai jiran gado ya yi, a lokacin wata hira da muryar Amurka. Yace a duk lokacin da shugaba ya bi kananan dokoki, shima dan kasa, talaka bashi da wata hujjar da zai karya doka, kuma a duk inda shugaba ya bi kananan dokoki to manyan ma baza su gagareshi ba.
Malam Usman ya kuma ce abinda ya kamata a gane shine, karya karamar doka irin wannan ka iya haddasa salwantar rayuwa. Ya kara da cewa a duk inda shugaba ya kiyaye kananan dokoki, babu shakka ba zai gaza ba wajen kiyaye manyan dokoki.
Wasu na ganin cewa daya daga cikin abubuwan da suka sa aka sami nasara wajen kisan tsohon shugaban kasar Najeriya Janar Murtala Mohammed a shekara aluf dari tara da saba’in da shida shine kiyaye doka irin wannan a lokacin da yake kan hanyarsa zuwa wajen aiki. Bayan haka ranar 23 ga watan Yulin shekarar da ta gaba shima Janar Buhari din an kai mashi hare a lokacin da yake kan hanya tare da tawagarsa a Kaduna.
Amma a cewar Malam Usman, akwai matakan tsaro dayawa da mukarabban shugaban zasu dauka wajen kare shi. Tun da dai shi yace zai bi dokar, to lallai ya san yadda zai yi kuma ma Allah zai kiyaye shi.
Ga hirar Malam Usman Ahmed Kabara da Usman Mohammed.