Kabilar karimjo sun ki amincewa da nadin domin a cewar su, sarautar garin ta Karimjawa ce ba ta Wurkunawa ba kasancewar garin Karim Lamido ba garin wurkun ba ne.
Kakakin Rudunar 'yan Sandan jihar Taraba SP Usman Abdullahi, ya tabbatar wa wakilin Muryar Amurka a Adamawa Salisu Lado Garba faruwar Rikicin kana a kalla mutane hudu sun mutu sannan an yi asarar dukiyoyi da dama wanda yanzu haka 'yan sandan jihar da kuma dakarun hadin gwiwa suna aiki tukuru domin ganin an shawo kan wannan Rikicin.
Wani mai fada a ji a masarautar ta Karim Lamido, Honorabul Tanko Babbo Andame kuma dan kabilar Wurkun, ya ce yanzu haka dai babu zaman lafiya a garin domin mutane suna gudun hijira suna barin garin domin ceton rayukan su.
Shi ma sarkin garin Monde da ke karamar hukumar ta Karim Lamido, Markus kantang ya yi wa Muryar Amurka bayanin yadda lamarin ya faru; inda yace sun rako sabon Sarkin gida sai 'yan banga suka fara harbe-harbe har cikin gidan sarkin. An dauko wanda aka fara harbinshi kafin daga bisani suka bada umurnin a fitar da shi waje, bayan nan ne kuma lamarin ya ta'azzara.
Shugaban karamar hukumar Karim Lamido na riko, Honorable Shehu Bibos ya ce yanzu haka dai mutane hudu ne suka riga mu gidan gaskiya sannan da dama kuma sun yi gudun hijira, an kuma kona gidaje sama da Sittin ko abin da ya yi kama da haka.
A saurari rahoton Lado Salisu Garba:
Your browser doesn’t support HTML5