Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Sabon Sarkin Zazzau: Ta Leko Ta Koma


Sarkin Zazzau Shehu Idris.
Sarkin Zazzau Shehu Idris.

Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa an sake lale a shirin zaben magajin marigayi Sarkin Zazzau Emir Shehu Idris.

A cikin sanarwar da Muyiwa Adekeye mai ba gwamnan jihar Kaduna shawarwari kan harkokin sadarwa ya rubuta, gwamnatin jihar ta ce wadanda hakkin zaben sabon sarki ya rataya a wuyansu zasu sake lale a shirin zaben sabon sarkin biyo bayan korafi da suka samu na rashin ba dukan masu sha’awar wannan kujera damar gabatar da wasikunsu.

Karin bayani akan:​ Sarkin Zazzau Shehu Idris, jihar Kaduna, Nigeria, da Najeriya.

Sakataren gwamnatin ya bada umarnin komawa a sake fara sabon zaman zaben sarkin ne bayan soke tsarin farko sabili da rashin sa sunayen wadansu ‘yan takara biyu da aka ce sun shigar da takardun neman kujerar a makare.

Mutanen biyu da suka gabatar da korafin wadanda dukansu suke rike da mukaman sarauta, da suka hada da Bunun Zazzau wanda ya yi korafin cewa bai sami damar shigar da takardar neman ba sabili da an ce mashi ya Makara, da kuma Sarkin Dajin Zazzau wanda ya yi korafin cewa, shima ba a bashi damar shiga jerin masu neman sarautar ba.

sarkin-zazzau-shehu-idris-ya-rasu

zaria-masarautar-zazzau-na-ci-gaba-da-zaman-makoki

Sanarwar ta kuma bayyana cewa masu zaben sarkin sun tantance ‘yan takara biyu ba tare da sun yi nazarin bayanan ayyukan da suka yi ba da aka gabatar masu kwana guda bayan sun tantance ‘yan takarar biyu.

Sanarwar da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar Balarabe Abbas Lawal ta bayyana cewa, masu zaben sarkin sun fara zaman tantance sunayen da aka gabatar, batun da gwamnan jihar Nasiru El-rufa’i ya jadada a sakon da ya kafa a shafinsa na twitter da ya hada da wasikar da aka fitar daga ofishin sakataren gwamnatin jihar.

Tuni dai mutane suka fara maida martani kan wannan batun a shafukan sada zumunta inda wadansu suke kushewa gwamnati domin jan kafa, yayinda wadansu kuma suke zargin gwanatin jihar da neman yin katsalandan a zaben sabon sarkin.

"Komi a Najeriya yana da wuya gwamnati ta gudanar. Sarki, Sheikh Shabah ya mutu a Kuwait, washe gari aka nada sabon sarki. Menene damuwarmu? Me ya sa ake jan kafa haka?@elrufai kana bukatar daukar mataki a kan wannan. Kada ka bari a bata maka suna."

Yanzu haka dai mutane goma sha daya ne ke takarar zama Sarkin Zazzau Shehu Idris na 19, matsayin sarautar mai daraja ta daya.

Mutane uku na farko da masu zaben sarkin suka fara kada kuri'a a kai sune: Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu daga zuriyar Katsinawa da Yariman Zazzau, Alhaji Muhammed Munnir Jafaru daga zuriyar Bare-bari da kuma Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris daga zuriyar Katsinawa.

Sauran masu neman sarautar sun hada da, Ahmad Nuhu Bammali (Magajin Garin Zazzau), Abdulkarim Aminu (Wanban Zazzau), Aminu Umaru Idris (Dangaladiman Zazzau), Bello Umaru Idris (Baraden Zazzau), Saidu Mailafiya (Ciroman Zazzau), Shitu Dikko (Dangaladiman Waziri Zazzau), Sambo Shehu Idris (Sarkin Kudun Zazzau), da Yusuf Shehu Idris (Sadaukin Zazzau

Sarkin Zazzau Mai Martaba Alhaji Shehu Idris ya rasu ne ranar 22 ga watan Satumba, yana mai shekara 84 a duniya bayan ya shafe shekaru 45 bisa karagar mulki. Sarkin ya yi bukin cika shekara 45 akan karagar mulki a watan Fabrairun wannan shekarar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG