Yayin da kwararru da manazarta ke ci gaba da bayyana hanyoyin warware kalubalen tsaron da sassan Najeriya ke fuskanta, Majalisar masarautar Gaya a jihar Kano na kokarin zaburar da masu rike da sarauta kan nauyin kare rayuka da dukiyar al’umomin gundumominsu, yayin da kwamishinan kananan hukumomi na jihar Jigawa yana cewa, kananan hukumomin na taka rawar gani game da batun tsaro a kasa. .
Sha’anin tsaro dai a Najeriya na daukar sabon salo kusan kullu yaumin, yayinda kasar ke tunkarar manyan zabukan shugabanni da za’ayi badi idan Allah ya kaimu.
Duk da aminci da zaman lafiya da ke wanzuwa a jihar Kano da makwafciyar Jigawa, masu ruwa da tsaki, musamman sarakunan gargajiya a jihohin biyu na cewa, suna daukar matakan dorewar zaman lumana a tsakanin al’umomin su.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake tsare-tsaren bada sandar girma ga sabon Sarkin Gaya Dr Aliyu Ibrahim a ranar asabar mai zuwa, wanda gwamnatin Kano ta nada bayan rasuwar mahaifin sa, kimanin watanni uku da suka shude.
Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji dake zaman Wazirin Gaya shi ke jagorantar kwamitin tsara taron.
Tanbihi kan harkokin tsaron shi ne zai mamaye taron laccar da za’ayi gabanin wannan rana.
Hakan dai na zuwa ne adai-dai lokacin da kwamishinan kananan hukumomi da sha’anin masarautu na jihar Jigawa Alhaji Kabiru Sugungu ke fayyace gudunmawar kananan hukumomi ga sha’anin tsaro a Najeriya.
Sai dai duk da haka, masu kula da lamura nada ra’ayin cewa, samar da cikakken ‘yancin kudade ga kananan hukumomi zai taka gagarumar rawa wajen dakile fitinar tsaro a Najeriya.