Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya fitar na cewa marigayi Shehu Malami wanda babban dan kasuwa ne kuma basarake ne wanda ya yi imani da tattalin arzika kasarsa.
Sanarwar ta ce za a ci gaba da tuna shi bisa irin gudunmuwar da ya baiwa kasarsa.
Sanarwar ta isar da sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin da majalisar Mai Alfarma sarkin Muslimi da kuma gwamnati da al'ummmar jihar Sokoto bisa wannan babban rashi.
Marigayi Shehu Malami wanda dan gidan sarauta ne, ya yi karatu a makarantu daban daban bayan kamamala karatun firamare a Sakkwato.
Ya yi makarantun gaba da firamare a Kano, Katsina, da Bidda.
Kazalika ya yi karatu a Ingila inda bayan dawowarsa Najeriya a shekarar 1963 ya taka rawa a harkokin kasuwanci sosai.
Shehu Malami wanda ya yi aiki a gidan rendiyon BBC, ya kuma zama sakataren firimiyan tsohuwar jihar Arewa sir Ahmadu Bello baya ga mukamai da ya rike a kamfanoni da bankuna da kuma sarkin Sudan na Wurno.
Kazalika ya kuma zama jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu a zamanin gwambatin soja ta marigayi Janar Sani Abacha.