Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Zamfara Ta Dakatar Da Wani Basarake Saboda Ba Dan Ta'adda Sarauta


Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Zamfara Dep Governor)
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Zamfara Dep Governor)

A Nigeria, gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin kasar ta dakatar da Sarkin Birnin ‘Yan Daton Tsafe Alhaji Aliyu Garba Marafa daga mukaminsa saboda yi wa kasurgumin dan ta'adda Ado Aliero nadin sarauta a matsayin Sarkin Fulanin Daji a ranar Asabar 17 ga watan Yuli.

ZAMFARA, NIGERIA - Gwamnan jihar, Dakta Bello Matawallen Maradun ne ya bada umarnin dakatarwar a yammacin ranar Lahadi, inda ya nisantar da gwamnatin jihar daga batun Nadin Aliero.

Sanarwar da sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe Sardauna ya bada, ta bayyana cewa gwamna Matawalle ya nada kwamiti mai mutane shidda a karkashin shugabanci Honarabul Yahaya Chado Gora, don ya binciki dalilin da ya sa Sarkin yin wannan nadin.

Sanarwar ta bayyana cewa, Alhaji Mahe Garba Marafa, hakimin ‘Yan Doton, shi ne zai gudanar da harkokin mulki a masarautar.

Nadin sarautar Aliero
Nadin sarautar Aliero

Tun da farko kafin a yi nadin sai da shugaban karamar hukumar Tsafe, Aminu Mudi Tsafe ya bayyana cewa Ado Aliero dan asalin Tsafe ne, kuma a baya bayan nan ya taimaka wajan samar da kwanciyar hankali bayan sulhun da aka yi, wannan ya sa mai girma Sarkin Birnin ‘Yan Doton ya ga dacewar a dora masa nauyin sarauta don ya kara tabbatar da zaman lafiya a daukacin masarautar baki daya.

“A bisa wadannan dalilan ne suka sa Sarkin ‘Yan Daton Tsafe ya amince da nadin Ado Aliero a matsayin Hardon Fulanin,” a cewar Mudi.

Nadin Aliero
Nadin Aliero

Wasu ‘yan asalin masarautar ‘Yan Doton, sun shaida wa Muryar Amurka cewa bayan sulhun, Aliero ya samar da zaman lafiya har an fara noma a gonaki a yankin, a cewarsu ta hanyar sulhu ne kadai za a samu zaman lafiya.

‘Yan bindiga da dama a kan babura ne dai suka halarci bukin nadin Sarkin Fulanin Daji Aliero.

Saurari cikakken rahoton Sani Shu'aibu Malumfashi:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:09 0:00
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG