Rikicin Isra’ila-Falasdinu: Biden Zai Kai Ziyara Isra’ila, Jordan

Biden/Blinken - Isra’ila/Hamas

Shugaban Amurka Joe Biden zai kai ziyara Isra'ila da Jordan ranar Laraba domin ganawa da shugabannin Isra'ila da na Larabawa, yayin da ake fargabar cewa yakin Isra'ila da Hamas zai iya kazance wa ya mamaye yankin.

WASHINGTON, D. C. - Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya sanar da ziyarar Biden zuwa Isra'ila a daidai lokacin da al'amuran jin-kai a zirin Gaza ke kara tabarbare wa kuma a daidai lokacin da Isra'ila ke shirin kai wani hari ta kasa kan yankin mai fadin murabba'in mil 141 (kilomita 365) domin kawar da kungiyar Hamas.

Gaza Strip, October 16, 2023.

Mayakan da ke da alhakin abin da jami'an Amurka da na Isra'ila suka ce shi ne hari mafi muni da aka kaiwa Yahudawa tun bayan kisan kiyashi na Holocaust.

Biden na da niyyar jaddada cewa har yanzu Amurka ta na goyon bayan Isra'ila yayin wannan ziyarar.

Gwamnatinsa ta Dimokradiyar ta yi alkawarin bayar da tallafin soji, inda ta kuma tura jiragen yakin Amurka da agaji zuwa yankin.

ISRAEL-PALESTINIANS/GAZA

Jami'ai sun ce za su nemi tallafi daga Majalisar Wakilai na sama da dala biliyan 2 a matsayin karin taimako ga Isra'ila da Ukraine, wacce ke yaki da mamayar Rasha.

Wannan wata dama ce ga Biden inda zai nuna ingancin tsare-tsarensa a fannin tsaro ga masu kada kuri’a a Amurka yayin da ya rage shekara daya a yi zaben 2014.

Haka nan wata dama ce ta nuna cewa yana cika alkawuran da ya yi a yakin neman zabensa inda ya ce zai sake farfado da kimar Amurka a idon duniya, bayan shekaru hudu da tsohon Shugaba Donald Trump ya yi yana assasa tsarinsa “na fifita Amurka” akan komai a fannin manufofin Amurka na waje.