Rigimar Iko a APC

  • Ibrahim Garba

Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa

Takaddamar iko da jam'iyyar adawa ta APC ta bayyana karara bayan kaddamar da wata jami'a a Sakkwato da ta tara jiga jigan 'yan APC tun daga nesa amma Bafarawa bai je ba.
Da alamar dai kaddamar da sabuwar jami’ar da aka yi a Sakkwato da kuma launin siyasar da kaddamarwar ta dauka ta bar baya da kura.

Da Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko na jihar ta Sakkwato da tsohon Gwamnan tsohuwar jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa, duk sun nisanta taron da siyasa amma kuma bisa dalilai daban daban kuma masu nuna rashin jituwa da juna a siyasance.

Alhaji Bafarawa, wanda jigo ne a jam’iyyar APC ya ce ba a gayyace shi wurin taron ba, duk kuwa da matsayin sa a jam’iyyar APC. Don haka ya ce idan kuwa da manyan ‘yan APC ake nema da an gayyace shi. Ya ce hatta ita kanta APC ta matakin jiha ba a gayyace ta ba. Don haka ya ce ba mamaki manyan bakin sun halarcin taron kaddamar da jami’ar ne saboda abotansu da Gwamna Wamako.

Da wakilinmu na Sokoto Murtala Faruk Sanyinna ya tambaye shi baya ganin rashin halartarsa taron na tabbatar da rade radin cewa akwai baraka tsakaninsu ganin yawancin jiga jigan APC daga wurare masu nisa sun je ga shi kuma shi a jihar ya ke? Sai ya ce zuwan Tinubu ko Bisi Sokoto sam bai da alaka da APC; kuma APC ba jam’iyyar mutum guda ba ne. Hasalima, yadda Tinuba ko Bisi ke da tasiri a APC haka shi ma ya ke da shi.

Shi ma Gwamnan Sokoto Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya nisanta taron da sha’anin siyasa. Ya ce ai akwai ‘yan APC da ‘yan PDP da wadanda ba ‘yan siyasa ba, da kuma ma wadanda ba ‘yan Nijeriya ba ne a wurin kaddamarwar. Ya ce hatta Shugaban Nijar ya turo wakilansa. To amma ya ce har yanzu ba a sasanta rigimar cikin PDP ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Rigimar Iko a APC - 3:00