Dubun dubatan 'yan PDP suka canza sheka zuwa jam'iyyar APC wadanda suka hada da manyan tsofofin jami'an gwamnatin da . Tsohon sakataren gwamnatin jihar Alhaji Mohammed Bawa Gusau shi ne ya jagoranci 'yan PDP din shiga APC a wani gagarumin taron yin maraba da gwamnan jihar ya shirya a Gusau.
A jawabinsa gwamnan jihar ya ce shugabanci yana dorewa ne bisa ga adalci. Ya ce abubuwan dake faruwa sun nuna cewa PDP bata yiwa 'ya'yanta da kasar adalci ba. Dole wadannan su faru. Ya ce abu ne na gaskiya kuma mutane sun shirya su canza domin su zabi kowanene suke so. Lokacin da ake danniya da yiwa mutane barazana ko ta halin kaka ya wuce. Yanzu jama'a su ne zasu zabi gwamnatin da suke so su dora kan karagar mulki.
To sai dai wasu shugaban PDP da suka ragu kamar Alhaji Sani Mohammed Anka ya ce duk wadanda suka tafi dama ba 'yan cikakkun jam'iyyarsu ba ne. Ya ce dama wa zai yi tafiya da matsolo. Ya ce tafiyarsu alheri ce ga PDP. Bayan sun tafi wasu da basa cikinsu sun dawo wurinsu. Ya ce su a Zamfara basu san ana rikici a PDP ba. Ya ce su a Zamfara basa cikin wannan rikicin.
Ga karin bayani daga Murtala Faruk Sanyyinna.