Bisa ga duk alamu tsugune bata kare ba ma PDP domin rikicin jam'iyyar yana son ya dauki wani sabon salo. Rincabewar rikicin ya fito karara domin maimakon tattaunawar da aka ce shugaban kasar Najeriya zai yi da gwamnonin nan bakwai da suka bijirewa jam'iyyar sai karin baraka ake gani. Kawo yanzu wani babban labari dake fitowa shi ne wadannan gwamnoni bakwai sun kammala shirin barin ita jam'iyyar PDP. Akwai raderadin cewa ko su shiga jam'iyyar APC ko kuma su kafa tasu. Abun da ya kawo wadannan rade radin shi ne kalamun wasu daga cikin gwamnonin.
Wasu gwamnonin sun ce idan ba'a samu sauyi ba kuma tafiya ta cije sai su bar PDP su koma wata. Kwana kwanan nan aka ji gwamnan jihar Adamawa, daya daga cikin 'yan tawayen na cewa idan tafiya ta cije kuma aka ki kawo gyara bisa ga abubuwan da suka ce basu kamata ba to ko basu da wata wata illa su canza sheka. Gwamna Murtala Nyako ya shaidawa tawagar APC da ta kai masa ziyara cewa shi da sauran gwamnoni shida da PDP ke kutuntawa sun shirya barin jam'iyyar muddin ba'a sake tsari ba.
Wasu masu kula da harkokin siyasa a Najeriya sun ce idan 'yan tawayen na hamkoron shiga jam'iyyar APC to menene zasu tsinta da babu shi a PDP domin dukansu 'yan Najeriya suka kafa su. Wasu kuma sun ce akwai daratsin da zasu koya wanda ka iya canzasu. Wasu kuma sun ce batun cewa zasu bar jam'iyyar PDP dabarar jaki ce. To sai dai Alhaji Adamu Abubakar wani mai kula da harkokin siyasa ya ce cikin gwamnoninnan bakwai akwai wadanda aka sansu da jajewa tun lokacin jam'iyyar PRP ta marigayi Malam Aminu Kano.
Malam Gali Sule mai sharhi kan siyasa ya ce idan wadannan gwamnonin suna son su kare martabarsu kuma abun da suke yi suna yi ne tsakaninsu da Allah to kafa tasu jam'iyyar ya fi masu. Amma muddin suka koma PDP ba tare da yin sauyin da suka bukata ba to kare ma sai ya fisu a jam'iyyar da ma kasar gaba daya. Su kare mutuncinsu su bar PDP domin su yiwa kansu kiyamar launi.
Sai dai wasu 'yan Najeriya sun yiwa gwamnonin kashedi cewa su yi hattara da gwamnatin tarayya. Su koyi daratsi da abun da ya faru da daya daga cikinsu wanda bai kwashe da dadi ba a hannun jami'an tsaro. Tun ma basu bar gwamnati ba ana muzguna masu to mai zai faru idan sun bari.Ya kamata su sha jinin jikinsu.
Ga karin bayani