Wannan hayaniyar da PDP ta shiga ta taimakawa APC ta numfasa daga irin matsaloli da take fuskanta. Daya daga cikinsu shine batun tantance wanda zai yiwa jam'iyyar takarar shugaban kasa, lamari da zai iya karo da muradun magoya bayan janar Muhammadu Buhari, mutuminda ya yiwa jam'iyyar adawa takara har sau uku. Akwai rade raden cewa ana kamfen na neman janar Buharin ya zakuda domin wani sabon jini ya yiwa jam'iyyar takara. Akwai kuma fargabar gwamnaonin da suke cikin sabuwar PDP suna dari-dari da janar Buhari, domin suna masa kallon bahagon mutum ne wanda yake daukan matakan babu sani babu sabo, har ana tunowa da zamanin mulkinsa na Buhari da Idiagbon a 1983.
Husseini Gariko tsohon dan hamayya ne tun zamnain NEPU. Ya gayawa Nasiru Adamu El-Hikaya cewa, hadakar jami'yun nan an kasu gida gida kuma kowa yana kare muradun mutuminda suke so ne. Yace akwai jita-jitar ma akwai wadanda suke neman akawarda janar Buhari daga kan takara domin suna da ajendarsu."idan ka kawarda janar Buhari daga kan takara, ka karya wannan jam'iyya a wajen talaka, domin ba zai zabeta ba". Ya ci gaba da cewa duk batagarin ba dominsu ake siyasar ba domin janar Buhari ne. Gariko yace idan aka kawarda janar Buhari daga takara, to sai dai idan za'a kyale janar Buhari ya fidda dan takara ya nunawa jama'a, amma muddin sune zasu fidda dan takara, to jama'a ba zasu zabi jam'iyyar ba. Mallam Husseini yace ko shi ba zai zabi jam'iyyar ba domin ba zai bata lokacinsa da na iyalainsa kan abunda ba za a sami nasara ba.
Husseini yace duk rigimar nan da ake yi a PDP daga karshen karshe duk zasu zo ne su hade suyi abu guda daya.Wannan ko shakka bana yi. Domin me, domin wasu yahudawa ne suka hadu wuri daya suke so suyi yahudancin su karya kasar, yansu suka raba kansu gida biyu don ace jam'iyyar ta rabu gida biyu, kariya ne inji Husseini Gariko jam'iyyar bata rabu gida biyu ba, a karshe sai sunzo sun hade su dinke domin ace an baiwa wasu hakuri.