Wadanda suka halarci taron bukin bude jami'ar daga bangaren jam'iyyar APC sun hada har da Janar Muhammadu Buhari, tsohon gwamna Bola Ahmed Tinubu na Jihar Lagos da shugaban riko na jam'iyyar Cif Bisi Akande.
Daga bangaren PDP-Sabuwa, akwai gwamna Rabi'u Musa kwankwaso na Jihar Kano, da gwamna Sule Lamido na Jihar Jigawa, da gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa da kuma gwamna Rotimi Amaechi na Jihar Rivers.
Da yake amsa tambaya a kan ko wadannan bangarorin biyu su na kokarin hadewa ne, janar Muhammadu Buhari ya ce uwar jam'iyyarsu ta APC zata bayar da sanarwa kai.
Shi ma gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso na Jihar Kano ya amsa tambaya a kan wannan batu inda yace har yanzu bangarensu na PDP-Sabuwa yana tattaunawa da bangaren PDP-Tsohuwa ta shugaban kasa da bamanga Tukur, kuma idan ba an gama tattaunawa ba, babu wanda zai ce ga inda za a dosa.
Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Abdulsalam Abubakar, shi ne ya ayyana bude Jami'ar ta Jihar Sokoto.
Murtala Faruk Sanyinna ya aiko da cikakken bayani daga Sokoto.