Ya fara da cewa shugaban kasar Najeriya na yanzu Goodluck Jonathan ya samu mulkin kasar ne cikin ruwan sanyi. Ya sameta ne kamar sadaka. Ba wani fafitika ya yi ba. Ta Ta fadi ne ya tsinta.Ya ce wadanda ya sa tare da shi da ma ministocinsa babu wanda ya san abun da yake yi. Ya yi misali da wadanda ya ce duk sun tsufa basu san abun da suke yi ba. Misali Edwin Clark wanda ya ce shi uba yake ga shugaban kasa bai san yadda aka ci zaben ba amma yau yana kan gaban masu cewa idan ba a bar Jonathan ya cigaba ba za'a yi tashin hankali. Tony Anenih shi ma yana babatu da bakinsa. Ya ce abun da su Atiku Abubakar suke yi ba su ba ne yin Allah ne. Ya ce idan Allah na son ya kawo canji sai ya yi.
Game da ko akwai hannun APC a rikicin PDP sai ya ce idan akwai hannu APC ai duk siyasa ce. Babu abokin gaba na dindindin ko abokin gaba na har abada a siyasa. Ya ce siysa sai ka yi da wanda baka so.Sai ka yi da barawo. Sai ka yi da mai kaya. Sai ka yi da mutumin kirki. Sai ka yi da dan iska domin kowane da ranarsa. Najeriya idan ba an yi canji ba an samu shugaba na gari babu cigaba. Ya ce kowa yake nagari shi yana so wato ko bayerabe, ko igbo, ko dan arewa amma idan ana son Najeriya ta zauna lafiya sai a kawar da shugabanci na yanzu.
Ya yabawa kakakin majalisar wakilan Najeriya Waziri Aminu Tambuwal wanda ya ce yana da ilimi, da hali na gari da iya shugabanci. Dan PDP ne amma shugaba ne mai kyau. Ya ce idan ya fito ko a PDP zai goyi bayansa.
Ga karin bayani