Ranar Lahadi Aka Cika Kwana 100 Da Fara Yaki Tsakanin Isra’ila Da Hamas

Lokacin da tankunan Isra’ila suka ratsa cikin Gaza

Afirka ta Kudu ta ce fiye da kasashe 50 ne suka nuna goyon bayansu ga shari'ar da ta gabatar a babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya da ke zargin Isra'ila da kisan kare dangi a kan Falasdinawa a yakin Gaza.

WASHINGTON, D. C. - Wasu, ciki har da Amurka, sun yi kakkausar suka ga zargin da Afirka ta Kudu ta yi na cewa Isra’ila na karya yarjejeniyar Majalisar Din kin Duniya kan Kariya da Hukuncin Laifukan Kisan Kare Dangi. Wasu kasashen da yawa sun yi shiru.

Isra’ila-Falasdinawa/Afirka ta Kudu-Kotun Duniya

Matakin da duniya ta dauka game da shari'ar da aka fara a ranar Alhamis da Juma'a da suka gabata, a kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, na nuni da rarrabuwar kawuna a duniya idan aka zo ga matsalar da Isra'ila da Falasdinawan suka shafe shekaru 75 suna fama da ita. Ranar Lahadi ne aka cika kwanaki 100 na rikicin da aka fi zubar da jini.

Wasu masu zanga-zangar goyon bayan Afirka ta Kudu a Kotun Duniya

Yawancin kasashen da ke goyon bayan shari'ar Afirka ta Kudu sun fito ne daga kasashen Larabawa da Afirka. A nahiyar Turai, Turkiyya kasar al'ummar Musulmai ce kawai ta fito fili ta bayyana goyon bayanta.

Turkiyya - Hagia Sophia

Babu wata kasar yammacin Duniya da ta bayyana goyon bayanta ga zargin da Afirka ta Kudu ta yi wa Isra'ila. Ita ma Amurka, abokiyar kawancen Isra'ila, ta yi watsi da batun a matsayin mara tushe, Birtaniya ta kira zargin mara gaskiya, kuma Jamus ta ce "ta yi watsi da shi."

Shugaban Amurka Joe Biden

Amma China da Rasha ba su ce komai ba game da abin da yake daya daga cikin manyan kararraki da aka gabatar a gaban kotun kasa da kasa. Tarayyar Turai ita ma ba ta ce komai ba.

-AP