Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbe Wasu ‘Yan Sandan Isra’ila Da Ake Zargin Kashe Wata Karamar Yarinya Bafalasdina


Sojojin Isra’ila
Sojojin Isra’ila

 ‘Yan sandan Isra’ila sun bude wuta kan wasu da aka zarga da afkawa da mota kan wani shingen binciken ababen hawa a yammacin kogin Jordan, tare da mummunan harbin wata kamar yarinya Bafalasdina dake cikin wata mota dake hannun riga da motar, a cewar ‘yan sanda da jami’an kiwon lafiya.

WASHINGTON, D. C. - An dai harbe wadanda ake zargin su biyu, yayin da wani matashin jami’in ‘dan sanda ya sami dan rauni. Lamarin da ya faru a yammacin jiya Lahadi, sa’oi bayan kisan mutane 9 a tashin hankalin da aka yi a yankunan Yahudawa ‘yan kama wuri zauna dake fama da karuwar tashe tashen hankulla, tun bayan barkewar yakin da Isra’ila ta kaddamar akan Hamas a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Jana’izar wasu Falasdinawa da aka kashe a Jenin
Jana’izar wasu Falasdinawa da aka kashe a Jenin

‘Yan sandan Isra’ilan sun ce, afkawar motar ya faru ne a wani wurin shingen binciken ababen hawa dake kusa da kauyen Biddu na Palasdinawa, daura da arewa maso kudu da birnin Kudus.

Hoton da kamarar tsaro ta dauka, ya nuna yadda wata farar mota tayi kukan kura ta afka kan wasu ‘yan sandan Isra’ila a wurin shingen binciken ababen hawar, inda daga nan ‘yan sanda suka dumfari motar a guje suka bude mata wuta.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG