Kamfanin dillancin Labaran Faransa na AFP yace daya daga cikin 'ma'aikatan sa yace an cigaba da lugudan wuta a Khan Younis da Rafah. Rafah dai yana kusa da kasar Misra kuma inda dubban Falasdinawa ‘yan gudun hijira suka nemi mafaka daga yakin.
A tsakiyar Gaza, Isra’ila ta kai hare haren sama a kan sansanin Nuseirat.
Ma’aikatar sojan Isra’ila ta ce ta lalata gidajen Hamas biyu a Beit Lahia a arewacin Gaza.
Rahotanni sun ce kashe kashe a Gaza ya biyo bayan da jami’an lafiya a Gaza suka ce an kashe kusan mutane 200 a cikin sa’o’I 24.
Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana fargaba a kan abin da suka ayyana shi da yunkurin auna ayarin ma’aikatan jin kai da sojoji Isra’ila suke yi.
Dandalin Mu Tattauna