Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fada Tsakanin Hamas da Isra'ila Ya Cigaba A Gaza


Rokokin da Isra'ila ta harba a Gaza
Rokokin da Isra'ila ta harba a Gaza

Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin Hamas da Isra'ila a Gaza bayan tsagaita wutar  kwanaki bakwai da aka yi, wanda ya taimaka wajen yin musayar fursunoni, da kuma shigar da kayan agaji a yankin da ya rugurguje.

Sabbin tashin hankalin na zuwa ne a daidai lokacin da wani rahoto na New York Times ya ce Isra'ila na da masaniya kan cikakken shirin Hamas na kai wa Isra'ila hari, amma aka yi watsi da shirin a matsayin "buri."

Kusan daftarin da aka fassara mai shafi 40, mai suna "Jerico Wall" wanda jaridar Times ta yi nazari, an yi cikakken bayani kan yadda Hamas za ta aiwatar da wani hari da yawa kan wuraren tsaron Isra'ila tare da kwace garuruwa. Ba a sanya ranar kai harin ba.

Jaridar Times ta ce sojoji da jami'an leken asirin Isra'ila sun san shirin fiye da shekara guda kafin harin na ranar 7 ga Oktoba. Ba a bayyana ko Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu shi ma yana da masaniya.

Babu wani martani da gwamnatin Isra'ila ta mayar kan rahoton Times.

A yayin da warin yaki ke komawa cikin Gaza, masu shiga tsakani na kasa da kasa na ci gaba da shawarwarin kawo karshen fadan.

IDF ta fada a dandalin sada zumunta na X, cewa ta yi nasarar katse makamin roka da aka harbo daga Gaza.

Sojojin IDF
Sojojin IDF

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin roka daga kungiyar Hamas.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta Hamas ta ce akalla mutane 32 ne suka mutu a cikin sa'o'i na farko na harin na ranar Juma'a.

Hamas
Hamas

Wani rahoto da jaridar New York Times ta fitar ya ce Isra'ila na da masaniyar cewa Hamas na da niyyar kai wa Isra'ila hari, amma Isra'ila ta yi watsi da shirin a matsayin "buri."

James Elder, mai magana da yawun UNICEF, ya ce a cikin wani bidiyo da aka saka a kan shafin X, daga asibitin mafi girma, da har yanzu yake aiki a Gaza cewa "Wannan asibitin ba shi da karfin da zai iya daukar karin yara masu raunukan yaki ." Ya ce bam ya fado "a zahiri kimaninn tazarar mita 50 daga nan."

Elder ya ce, "Rashin sa baki na masu hannu da shuni ne ke ba da damar kashe yara, wannan yaki ne kan yara."

Komawa fadan na zuwa ne bayan tsagaitawar kwanaki bakwai da ta bada damar musayar mutanen da Isra'ila ta yi garkuwa da su daga harin da Hamas ta kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba don fursunonin Falasdinu.

A ranar Alhamis din da ta gabata, kungiyar Hamas ta saki wasu Isra’ilawa 8 da aka yi garkuwa da su a Gaza a karkashin tsawaita tsagaita bude wuta, kuma jim kadan bayan haka Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa 30 a daidai lokacin da masu shiga tsakani suka yi kokarin sake tsawaita lokacin yakin.

An sako mata biyu da rana, wasu shida kuma an sake su jim kadan kafin tsakar dare. Wannan dai shi ne rukuni na bakwai da aka yi a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi tsakanin Hamas da Isra'ila.

Da farko dai Isra'ila ta bukaci kungiyar da ta saki akalla mutane 10 da aka yi garkuwa da su a kowace rana domin a ci gaba da tsagaita bude wuta, amma mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Qatar ya ce ba za a sake sakin wasu mutanen da aka yi garkuwa da su ranar Alhamis ba. Qatar ta taimaka wajen sasanta rikicin.

Kakakin na Qatar ya ce Isra'ila ta karbi mutanen takwas da aka yi garkuwa da su, saboda a ranar Larabar da ta gabata ne kungiyar Hamas ta saki karin wasu mutane biyu, wadanda mata ne 'yan asalin Isra'ila-Rasha.

Hamas ta yi nuni da cewa za ta iya 'yantar da wasu 'yan kasar Rasha, ‘yan asalin kasar Isra'ila- biyu, amma a karshe kungiyar ba ta yi hakan ba. Ita ma Hamas a baya ta ce za ta saki gawarwakin Isra'ilawa uku da aka yi garkuwa da su a yau Alhamis, amma babu tabbas ko hakan ta faru.

Ita kuma Isra'ila ta saki Falasdinawa 30 daga gidajen yari a Isra'ila.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG