Rabawa Marasa Aikin yi da Mabukata Kudade

Shirin Gwamnatin Najeriya, na rabawa marasa aikin yi da mabukata Naira dubu biyar biyar tafkar fadada shirin yaki da talauci ne da wasu jihohi suka taba yi daga 1999.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Oshinbajo, da ya bayana haka a taron yaye daliban na Crescent dake Abeokuta, a jihar Ogun kamara yadda jaridar Leadership ta ruwaito, Gwamnati, zata sabunta hanyoyin da tallafi ke isa hannun al’uma wanda daga nan ne za’a raba kashin farko na tallafin.

Oshinbajo ya nuna damuwa da cewa ‘yan Najeriya miliyan dari da ashitin da daya na fama da matsanancin talauci wato yaruwa da samun kwatankwacin Naira dari ukku .

Wani da APC, Sabo Imamu yace shirin na da kyau, amma da baiwa talakawa dauki na kudi gara a tallafa masu ta hanyoyin shigowar kudin, ya kara da cewa a rayuwa irin ta dan Najeriya, kuma mutanen karkara wadanda kudi nada kima da tasiri a wajen su wani yana samu dubu biyar a wata ina gabbatar maka sana’ar ba zai yi ba numar ma kuma bazai yiba zai zama cima zaune.